Tuesday, 17 September 2019

An ragewa Neymar dakatarwar buga wasannin Champions League daga 3 zuwa 2

Kotun wasannin ta CAS ta ragewa tauraron dan kwallon PSG Neymar yawan dakatarwar wasannin da aka mai daga 3 zuwa biyu sanadiyyar kalaman batancin daya gayawa alkalin wasa a kakar wasan data gabata.Bayan da aka yankewa Neymar hukuncin dakatarwa daga buga wasanni uku, PSG ta daukaka kara inda a yanzu wasanni 2 ne bazai buga ba watau wanda PDG din zata yi da Real Madrid da wanda zata yi da Galatasary.

Neymar dai ya zagi alkalan wasane a wasan da Manchester United ta fitar dasu daga gasar Champions League da aka yi bara.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment