Sunday, 15 September 2019

An Sake Sako Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihar Katsina

Yau ma cikin iko da yardar Allah, a karkashin shirin sulhu da sasanci da Gwamna Aminu Bello Masari yake jagoranta da masu hare haren ta'addanci da satar mutane, an sami amso mata goma sha biyar (15) da yara goma sha biyar (15) wadanda suka fito daga kananan hukumomin Kankara da Jibia.


A cikin jawaban shi, Alhaji Aminu Bello Masari yayi kira ga al'umma da aci gaba da addu'o'in Allah Ya kawo mana karshen wannan ibtila'in, domin duk wanda zai kama irin wadannan mutanen ya tsare har sama da kwana hamsin to hakika yana cikin wani yanayi da bamu taba gani ba a nan kasar.

Ya kuma yi kira ga wadanda aka sako din da su dauki abinda ya same su a matsayin kaddara kuma jarrabawa daga Allah Madaukakin Sarki.
Rariya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment