Sunday, 15 September 2019

Arsenal ta buga 2-2 da Watford

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta buga 2-2 da Watford a gasar cin kofin Premier da suka yi na yau Lahadi. Arsenal ce ke kan gaba da kwallaye 2-0 kamin a tafi hutun rabin lokaci saidai bayan dawowa Watford ta rama duka kwallayen aka tashi wasan 2-2.Aubameyang ne ya ciwa Watford kwallayenta saidai bayan dawowa daga hutun rabin Lokacu Watford ta dawo da wani karfi na musamman inda ta rufa Arsenal a gaba ta ko ina ba sauki, dan wasan Arsenal, Sokratis wajan buga kwallo sai ya je ya baiwa dan wasan Watford kwallon wanda hakan ya sa aka ci su.

Hakanan shima David Luiz ya jawowa Arsenal din bugun daga kai sai gola wanda shima aka cisu dashi.

Watford ta kaiwa Arsenal hare-hare har guda 31 a wasan, wanan shine yawan hari mafi yawa da aka taba kaiwa Arsenal hakanan itama Watford wannan shine hari mafi yawa data taba kaiwa wata kungiya.

Kamin Aubameyang ya ci kwallonshi ta biyu saida Arsenal ta taba kwallon sai 20, wannan ne taba kwallo mafi tsawo daga kawo sanadin ci kwallo a kakar bana, hakanan rabon da Arsenal ta ci wata kungiya kwallaye 2 sannan kuma kungiyar ta zo ta ramasu tun shekarar 2016 da suka buga 3-3 da West Ham.

An ci Arsenal kwallaye da bugun daga kai sai gola har guda 10 daga kakar wasan data gabata zuwa yanzu in banda Brighton babu kungiyar da akawa irin wannan cin a Premier League.

Da yake hira da manema Labarai bayan wasan, Xhaka ya bayyana cewa sun tsorata da Watford bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment