Friday, 13 September 2019

Ba Na Son Auren Saurayi Sai Mai Mata Daya, Biyu Ko Uku>>Hauwa Waraka

Jarumar Fina-finan Hausa ta Kannywood Hauwa Waraka da ta shahara a fitowa a matsayin tsagera ta bayyana Sha'awar ta na auren mai mata biyu ko uku. 


A yayin tattaunawar ta da Kamfanin sadarwa da yada labarai na SIRRINSU MEDIA an tambayi Hauwa Waraka cewa,  "Ba kya ganin Matan aure za su yi  fargabar yin kishi dake saboda Iya kissa da kisisinar ki? 

"Ba haka ba ne ni dai na san zan kula da mijina na nuna masa soyayya Iya soyayya"

Za ki Iya zama Da kishiya? 

Kwarai kuwa, ai ba zan zama kwarkwasa fidda giji ba na samu mace a gidanta da 'ya'yan ta kuma na kore ta?

Yaya batun auren mai mata?

"A ra'ayina Zan shiga a matsayin ta biyu ko ta uku ko ta hudu bana son auren mara mata....

Domin jin ragowar hirar ka inda za a danna Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment