Friday, 13 September 2019

Ba za mu kara wa ’yan Najeriya radadin talauci ba>>Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya ba za ta ka jefa ‘yan Najeriya cikin halin kunci da talaucin da su ke fama da shi ba.


Maimakon haka inji Buhari, Gwamnati za ta ci gaba da laluben hanyoyin da za ta rage da mabance wa jama’a radadin kunci da wahalhalun da su ke fama da su.

A kan karin kudin fetur

“A kan karin kudin fetur, na yarda da ku cewa akwai bukatar a kakkabe cin hanci da rashawa da kuma harkallar da ta dabaibaye fannin harkokin mai. To ina tabbatar muku da cewa wannan gwamnati ba ta da wata niyya ko fatan kara wa jama’a kunci da wahalhalu fiye da wadanda suke fama da su.”

Haka Buhari ya bayyana wa sabbin Shugabannin Haddiyar Kungiyoyin Kwadago (TUC, a karkashin shugaban su Quadri Olaleye, a Fadar Gwamnati, Abuja.

Buhari ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya na kan bakan ta na kari mafi kankantar albashi, tare da nuni da cewa taron Majalisar Zartaswar da aka gudanar jiya Laraba sai da ya tattauna tsare-tsaren da za a bijiro da zu na kusa da na nesa, wanda ya hada da batun karin albashi.

Buhari ya ci gaba da bayyana wasu nasarori da gwamnatin sa ta samar a farkon zangon mulkin sa, tare da yin magori wasa kan ka da kan ka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment