Tuesday, 10 September 2019

Babana yana min fyade kuma na gayawa mamana amma bata ce komai ba>>Inji yarinya 'yar shekaru 14

Wata yarinya 'yar shekaru 14 ta bayyana yanda mahaifinta ya rika mata fyade kuma ta gayawa mahaifiyarta amma mahaifiyar bata dauki mataki ba.
Yarinyar da ba'a bayyana sunanta ba ta gayawa jami'an Civil Defence a Legas cewa  mahaifinta yana mata fyade kuma ta gayawa mahaifiyarta, Mrs. Florence Ifelaka amma bata ce komai ba.

Tace koda a watan Augustan daya gabata saida ya mata fyaden lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya kuma da ta dawo ta gaya mata amma bata ce komai ba.

Florence ta bayyana cewa tun a shekarar 2016 diyartata ta taba gaya mata cewa mahaifinta na cin zarafinta amma ta dauka karya take, tace daga baya data wa mijin magana sai yayi barazanar yin maganinsu idan suka sake maganar ta fita.

Tace abu na karshe daya faru shine na Watan Agustan daya gabata inda taje ta gayawa 'yar uwarta shine 'yar uwartata ta kai kara wajan jami'an tsaro.

Chinedu Ifeleka dan shekaru 46 ya amince da laifin yiwa 'yarshi fade inda yace giyace daya sha ta jawo wannan abu kuma sau daya kawai yayi a watan Agusta.

Jami'in Civil Defence din yace zasu mikashi gurin hukumar dake kula da cin zarafin mata dan daukar mataki akanshi.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment