Sunday, 8 September 2019

Babu jirgin da yayi hadari da Mahajjata 600>>inji Hukumar kula da aikin hajji

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya, NAHCON a takaice ta bayyana cewa rahotannin da suka watsu jiya na cewa jirgi dauke da mahajjata sama da 500 yayi hadari yayi saukar gaggawa a filin sauka da tashin jirage na Jihar Naija ba gaskiya bane.Da yake mayar da martani kan lamarin daga kasar Saudiyya bayan da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya tuntubeshi, shugaban NAHCON, Alhaji Abdullahi Muhammad ya bayyana cewa labarin ba da gaske bane dan kuwa yana samun wannan labari ya daga waya ya kira dan yaji yanda lamarin ya faru kuma an tabbatar mai cewa ba gaskiya bane.

Ya kara da cewa har wasu daga cikin fasinjojin jirgin an yi magana dasu amma sun bayyana cewa su basu ma san da labarin ba.

Hakanan me kula da ayyukan kamfanin na Max Air, Captain Ibrahom Dili ya bayyana cewa, labarin ba gaskiya bane, abinda ya faru shine a lokacin da jirgin ya zo zai sauka dai aka samu gurbatar yanayi ta yanda na'urar da zata taimakawa matukin jirgin wajan saukeshi kasa ta samu matsala.

Dan haka direban jirgin yayi amfani da basurarshi wajan sauke jirgin da kanshi, dalilin hakane sai jirgin ya makale akan hanyar da yake gudu har injin jirgin ya bugi kasa ya samu matsala. Yace dalilin samun matsalar injin jirgin kenan amma ba wai a sama matsalar ta auku ba.

Ya kara da cewa, daga baya an ja jirgin zuwa inda fasinjoji suka sauka.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment