Wednesday, 11 September 2019

Ban yadda da hukuncin kotu ba zan daukaka kara>>Atiku

Bayan da shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi nasara akan Atiku Abubakar da PDP a kotu a yau Laraba inda kotun ta yi watsi da korafin da Atikun ya shigar na kalubalantar nasarar Buhari, Atikun yace be yadda ba zai daukaka kara.Da yake magana bayan yanke hukuncin, Lauyan Atiku, Mike Ozekhome ya bayyana cewa maganar daukaka kara ma dole ne su daukaka kara.

Itama jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ta kadu da sakamakon kotun inda tace duk da hujjoji masu kwari da ta gabatar na cewa Buhari be cancanci yin takarar shugaban kasa ba sannan kuma yayi aringizon kuri'a amma kotu ta bashi nasara.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment