Monday, 9 September 2019

Barcelona na kokarin baiwa Messi damar zama a kungiyar har abada saidai watakila ya koma Amurka da wasa

Wasu rahotanni dake fitowa daga kasar Sifaniya na cewa tauraron dan kwallon Bacelona, Lionel Messi ka iya komawa kungiyar MLS ta kasar Amurka wadda ke karkashin jagorancin tsohon tauraron dan kwallo,David Beckham.Kafar labaran kasar Sifaniya, Mundo Deportivo ce ta ruwaito da wannan labari.

A makon daya gabatane dai kungiyar ta Barcelona ta tabbatar da cewa Messi na da damar da zai iya barin kungiyar a duk sanda yaso domin hakan na kunshe cikin kwantirakin daya sakawa hannu.

A kwanakin bayane aka ruwaito Beckham na fadin cewa kungiyar tashi zata iya kawo Messi ko Ronaldo nan gaba ya buga mata wasa.

Saidai Mundo ta kara da cewa a yanzu Barcelonar tana shirin baiwa Messi wata dama ta musamman inda zasu bashi kwantirakin amincewa ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa lokacin da zai yi ritaya.

Koma dai ya zata kasance, lokaci be bar komai ba.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment