Sunday, 15 September 2019

Barcelona ta lallasa Valencia 5-2

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa Valencia da ci 5-2 a wasan da suka buga jiya na neman cin kofin Laliga. Suarez da De jong da Fati da Pique ne uka ciwa Barca kwallayen.Suarez yaci kwallaye 2 ne kuma hakan yasa ya kafa tariin kasancewa dan kwallo na farko da aka sako daga baya daya ciwa Barcelona kwallaye 2 tun bayan da Neymar yayi hakan a shekarar 2014 a wasansu da Athletic.

Hakanan Ansu Fati dan shekaru 16 ya kasance dan kwallo mafi karancin shekaru a gasar Laliga da yaci kwallo da kuma bayar da taimako a ci kwallo duk a wasa daya. Yanzu Fati yana da kwallaye 2 kenan a wasanni 3 daya buga. A lokacin da Messi ya fara kwallo yana matasgi said ya buga wasanni 13 kamin ya ci kwallo 2.

Frankie De jong yayi kokari sosai a wasan inda duka kwallayen da ya bayar sau 41 sun kai kan kafafun wanxa ya baiwa, be barar da ko daya ba sannan kuma ya kwace kwallaye 3 a wasan na yau.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment