Thursday, 5 September 2019

Bayan harin kyamar baki, 'yan kasar Afrika ta kudu sun sake tsokanar Najeriya

Bayan harin kyamar baki dake gudana a kasar Afrika ta kudu wanda ya shafi 'yan Najeriya har wasu suka fara tunani da daukar matakin ramuwar gayya, 'yan kasar ta Afrika ta kudu sun kuma sake tsokanar 'yan Najeruyar da wani sabon salon abu.Cikin masu tunain mayarwa da kasar Afrika ta kudu martani akwai wanda suka rika fatan dama Boko Haram ta shigarwa Najeriya ta kaiwa Afrika ta kudun hari.

Bayan wannan kuma wani labarin da baida asali ya rika yawon cewa wai Boko Haram din ta gargadi kasar Afrika ta kudu kan ta daina kaiwa 'yan Najeriyar hari.

Watakila wannan ne yasa a yanzu matasan kasar Afrika ta kudun suka fara wani salon shiga irin ta Boko Haram suna rike abubuwan dake kama da Bindiga suna dorawa akan shafukan sada zumunta inda suke amfani da taken "BokoHaramChallenge" cikin yanayin barkwanci.

Wannan abu ya dauki hankula sosai a kasar ta Afrika ta kudu inda ya zama na daya da aka fi tattaunawa akanshi a Shafin Twitter.

Ga kadan daga cikin irin hotunan da 'yan kasar Afrika ta kudun suke sakawa:Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment