Friday, 13 September 2019

Bayan tilastawa 'yan Najeriya suka dawo gida, 'yan kasar Afrika ta Kudu sun durfafi shagunan 'yan kasar Pakistan mazauna kasar

Bayan hare-haren suka kaiwa 'yan Najeriya da suka tilasta wasu komowa gida, Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan kasar Afrika ta kudu a yanzu kuma sun koma kan 'yan kasar Pakistan inda suka kai musu hari suna daka musu wawa a shagunansu.Wani bidiyon da ya watsu a shafukan sada zumunta ya nuna yanda 'yan kasar ta Afrika ta kudu a Ranar Larabar data gabata suka dakawa wasu shagunan 'yan kasar Pakistan wawa sai dai an ga masu shagunan suna dukan masu musu satar.

Hakanan an ga wani dan sanda a wajan saidai mutane sun sha karfinshi ya kasa Kula dasu.

Me magana da yawun 'yansanda, Brig Leonard Hlathi ya bayyana cewa an kama wasu da suka kai harin tare da kwato wasu daga cikin kayan da suka sata.

Kalli bidiyon yanda lamarin ya faru:

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment