Sunday, 8 September 2019

Bilkisu Shema ta sanar da mutuwar kawarta,Saidai kawar tace tana nan bata Mutu ba

Tauraruwar fina-finan Hausa, Bilkisu Shema ta bayyana a shafinta na Instagram cewa wata abokiyarta me suna, Hafsat Lere ta mutu, saidai Hafsat din ta fito tace tana nan da ranta.
Tun bayan saka labarin na Shema inda ta wa kawar tata fatan samun Rahamar Allah da kuma cewa ta yafe mata wasu suka fara cewa ba da gaske bane Hafsa na nan da ranta.

Hafsat din daga baya ta fitar da sanarwa ta shafinta na Instagram inda ta bayyana cewa matsala ta samu ta fadi kuma har a gidansu ansha ta mutu, ta kara da cewa ta gode da soyayyar da aka nuna mata.

Muna fatan Allah ya sauwake.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment