Saturday, 14 September 2019

Boko Haram Sun Kashe Shugaban 'Yan Kato Da Gora A Jihar Borno

Bayan hari da suka kai jiya a garin Gubio, mayakan na Boko Haram sun hallaka mutane da dama ciki har da Shugaban Civilian JTF wanda aka fi sani da kato da Gora na karamar hukumar Gubio na Jihar Borno. Wannan kisar dai da Boko Haram tayiwa wa Kwamandar CJTF ta bakantawa Al'ummar wannan yanki rai ganin yadda ake masa lakabi da (Maradona) saboda jajircewa wajen kare Al'ummar Wannan yanki! 

Tuni aka yi jana'izar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Ku saka shi cikin addu'o'inku 'yan uwa. Allah ya jikansa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment