Sunday, 8 September 2019

Boko Haram sun wa sojoji kwacen Kudi da kayan aiki

Rahotannin dake fitowa daga jihar Borno na bayyana cewa mayakan Boko Haram sunwa sojojin Najeriya kwacen makudan kudi da motar yaki a yayin da suke kan hanyar zuwa Maiduguri daga Yobe.Premiumtimes ta ruwaito cewa sojojin na kan hanya sunje daidai Azare-Kumaya sai mayakan Boko Haram din da suka musu kwantan Bauna suka afka musu, bayan bata kashi suka kwace wasu kayan da suke dauke dasu tare da barin soja daya cikin rauni.

Lamarin ya farune ranar Juma'ar data gabata.

Daga cikin abubuwan da suka kwace daga hannun sojojin akwai kudin alawus da za'a biya sojojin da suka kai Naira miliyan 15 wanda ake biyan sojojin dubu 1 duk rana.

Har zuwa yanzu dai Hukumar sojin bata fitar da sanarwa akan wannan lamari ba.

Karin sojoji da aka tura wajan sun kashe daya daga cikin 'Yan Boko Haram din saidai kamfanin dullancin labarai na AFP yace Boko Haram ta yi ikirarin kashe sojoji 2 a harin


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment