Wednesday, 11 September 2019

Buhari: Kotu ta yi watsi da karar Atiku

Kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, yana kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.


Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari'a Muhammad Garba ta tabbatar da Shugaba Buhari na jam'iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben watan Fabrairun 2019.

Sakamakon da hukumar zaben kasar, INEC, ta fitar ya nuna cewa Shugaba Buhari, mai shekara 76, ya samu kuri'a miliyan 15 da dubu 200 yayin da Alhaji Atiku Abubakar, mai shekara 72, na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a miliyan 11 da dubu 300.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment