Wednesday, 11 September 2019

Buhari ya cancanci ya yi takara>>Kotu

Kotu ta ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai cancanci ya tsaya takara ba saboda bai je makaranta ba.


Daya daga cikin korafe-korafen da PDP da Atiku suka gabatar a gabanta shi ne cewa Buhari ba shi da takardun shaidar zuwa makaranta sabda haka bai cancanci ya yi takarar ba baki daya.

Kotun ta ce dokar zabe ba ta tilasata wa dan takara ya hada da takardun shaidar kammala karatunsa ba yayin mika fom mai lamba CF001 kafin a tabbatar da cancantarsa.

Mai Shari'a Muhammed Garba ya ce Atiku da jam'iyyarsa ta PDP sun gaza gamsar da kotu cewa takardun da Buhari ya gabatar ba na gaskiya ba ne.

Sannan kuma sun yi zargin cewa Buharin ya yi karya game da takardun shaidar kammala karatunsa, abin da kotun ta yi watsi da shi domin, a cewarta, tun kafin zabe ya kamata a duba shi ba bayan zabe ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment