Friday, 13 September 2019

Chelsea da Real Madrid sun aje alkawari kan N'golo Kante

Rhotanni daga Sifaniya da Daily Express ta samo sun bayyana cewa kungiyar Real Madrid da ta Chelsea sun samu fahimta da ajiye alkawari akan dan wasan Chelsean, Ngolo Kante.Rahoton yace saboda dadin huldar da suka yi kan sayen Eden Hazard, Chelsea ta wa Madrid Alkawarin cewa ifan ta tashi sayar da Kante zata mata magana.

Chelsea dai ta siyo Kante ne daga Leicester Bayan da ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Premier League kuma Kanten ya kafa tarihin kasancewa dan kwallon Premier na farko daya ci kofin na Premier da kungiyoyi biyu sau biyu a jere.

Saidai har yanzu Kante be warware daga ciwon da taji ba dan kuwa ba zai buga wa kungiyar wasan da zasu yi da Wolves ba gobe kamar yanda kocin kungiyar Lampard ya nunar.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment