Saturday, 14 September 2019

Chelsea ta lallasa Wolves 5-2: Tammy Abraham ya kafa muhimman tarihi hadda irin na Ronaldo

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta lallasa Wolves da ci 5-2 a wasan da suka buga na gasar cin kofin Premier League na wannan satin, inda matasan 'yan wasanta, Tomori ya fara cin kwallo daya sai kuma Tammy Abraham da ya ci kwallaye 3 ringis shi kadai sai kuma Mason Mount da ya ci kwallo daya.Duk da kwallayen da ya ci,Abraham ya kuma ci kungiyar tashi ta Chelsea kwallo daya bisa kuskure sai kuma Cutrone da ya ciwa Wolves kwallo ta biyu, haka aka tashi wasan da sakamakon 5-2.

Tammy Abraham ya kafa tarihin zama dan kwallon Chelsea na farko mafi karancin shekaru da ya taba ci mta kwallaye 3 a wqsa daya, sannan kima shine na 72 daya ci mata kwallaye 3 a wasa daya, an ciwa Chelsea kwallaye  a wasa daya sai 149 a tarihinta.

Kuma shekaru 3 kenan a jere, tun shekarar 2017 da 'yn wasan Chelsea suke ci mata kwallaye 3 a wasa daya cikin watanin September.

Abraham a yanzu yana da kwallaye 7 kenan a wasanni 3 daya bugawa Chelsea kuma a yanzu babu wanda ya kaishi cin kwallo a gasar Premier League. Sai Aguero da yaci kwallye 7 amma a wasanni 5.

Duka kwallayen da aka ciwa Chelsea a gasar Premier League ta bana watau 11 duk matasan 'yan kwallon da suka fito daga makarantar horas da 'yan kwallon tane da basu wuce shekaru 21 da daya ba watau Abraham, Mount da yaci kwllaye 3 da Tomori da yaci 1, banda kwallon da Abraham ya cita bisa kuskure, babu kungiyar Premier League data taba yin haka.

Hakanan Tammy Abraham ya kafa irin tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa lokacin yana Manchester United da wanda Dele Alli na Tottenham ya kafa na kasancewa dan shekaru 21 ko kasa da aka daya jera wasanni 3 yana cin kwallaye fiye da daya.

Akanan kwallon da yaci Chelsea bisa kuskure ta sa Abraham ya kafa tarihin asanceea dan kwallon Premier League na farko daya ci kwlalaye 3 sannan kuma ya ci kungiyarshi kwallo a wasa daya.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment