Monday, 9 September 2019

Cikin dalibai miliyan 1.6 da suka rubuta JAMB 443,624 ne kawai suka samu shiga jami'a

Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta JAMB ta bayyana cewa cikin dalibai sama da miliyan 1.6 da suka rubuta jarabawar shiga jami'a a shekarar 2018 data gabata guda 443, 624 ne kawai suka samu shiga makarantun gaba da sakandire.
Wannan na kunshene a cikin rahoton da JAMB ke fitarwa duk sati inda ya nuna cewa jami'o'in Najeriya nada gurbin karatun dalibai 143, 338 da ba'a cike ba a shekarar data gabata hakanan kwalejin kimiyya suma suna da nasu guraben daliban da ya kamata a dauka amma ba'a dauka ba.

JAMB tace dalilin rashin cike wadannan guraben shine daliban basu da yawan maki ko kuma irin sakamakon jarabawar da ake bukata.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment