Wednesday, 18 September 2019

Da gaske Buhari ya ragewa Osinbajo mukami?Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kaddamar da majalisar bai wa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki.Hakan ya biyo bayan rushe kwamitin tattalin arzikin kasar, wadda mataimakin shugaban kasar Professor Yemi Osinbajo ke jagoranta.

Yayin da wasu ke cewa sambarka, wasu dai na kallon matakin a matsayin yunkurin rage ikon mataimakin shugaban kasar.

Amma a tattaunawarsu da Ibrahim Isa, mai taimaka wa shugaban kasar kan harkar yada labarai, Mallam Garba Shehu ya ce ba haka lamarin yake ba.Garba Shehu ya ce an kafa wannan majalisar ce kamar yadda ake da masu bayar da shawara a fannoni daban-daban na harkokin kasa.

Ya ce "Wannan kwamiti idan ya zauna ya tattauna ya bayar da shawar, shugaban kasa za a bai wa, kuma shugaban kasa da mataimakinsa duk daya ne."

Kuma a cewarsa ana sa ran wannan kwamiti zai taimaka wajen magance irin matsalolin da tattalin arzikin kasar ke fama da su.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce kwamitin tsaro da ake da shi a baya ya yi bakin kokarinsa a bangaren tattalin arziki.

Amma a acewarsa gwamnati ta ga cewa lokaci ya yi da za a sauya dabara.
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment