Monday, 16 September 2019

Dan Najeriya da aka zaba shugaban majalisar Dinkin Duniya zai fara Aiki

Wakilin Najeriya a majalisa dinkin Duniya, Farfesa Tijjani Muhammad Bande da aka zaba a matsayin shugaban majalisar zai fara aiki akan sabon mukamin nashi a ranar 16 da 17 ga watannan na Satumba da muke ciki.
Farfesa Tijjani zai fara aikinnne gabanin taron kasashen Duniya da za'a yi kwanannan. Dama ya taba zama mataimakin shugaban majalisar a shekarar 2016, dan Asalin jihar Kebbi yayi makaranta a jami'ar ABU Zaria da jami'o'in Boston da Tronto.

Me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyanawa cewa Najeriya zata aike da wakilai na musamman dan su shaida wannan muhimmiyar rana ta kafa tarihi,Wanda zasu wakilci Najeriyar sune Shi malam Garba Shehun sai, ministan harkokin kasashen waje, Geofrrey Onyeama sai shugaban ma'aikatar tattara bayanan sirri na kasa, Ahmad Rufai.

Farfesa Tijjani zai kasance a wannan matsayine har tsawon shekara daya kuma zai taimaka wajan kawar da matsalolon da ake fama dasu a Duniya itin su tsaro da kawar da yunwa da samar da ilimi da cimma muradun karni dan kuma dumamar yanayi, kamar yanda sanarwar Garba Shehu ta bayyana.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment