Friday, 13 September 2019

Dan shekaru 35 ya yi garkuwa da kanshi dan ya damfari mahaifinshi Naira dubu 500

Wani mutum dan shekaru 35  me suna Hamza Abdullahi ya hada baki da abokin Auwal Shu'aibu ja zace kanahi dan ya damfari mahaifinshi kudi Naira dubu 500.
Lamarin ya farune a babban birnin tarayya, Abuja inda aka kama Hamza a Katampe yayin da yazo karbar kudin fansar da za'a biya akansa.

Hamza ya bayyanawa The Nation cewa daya daga cikin 'yansandan da aka zo dasu biyan kudin fansar ne ya ganeshi saboda yana tunain mahaifinshi ya nunawa 'yansandan hotonshi.

Yace yaso ya damfari mahaifin nashi kudinne dan ya biya kudin haya da sauran wasu bukatu.

'Yansandan Abuja sunce akwai mutum daya da suka yi wannan aika-aika tare da ake nema

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment