Friday, 6 September 2019

Dan shekaru 49 yawa 'yar shekaru 15 fyade bisa amincewar mahaifiyarta

Jami'an 'yansandan jihar Edo sun kama wani mutum me shekaru 49 da yawa 'yar shekaru 15 fyade bisa amincewar mahaifiyarta.




Mutumin me suna Mr Raphael wanda yarinyar Agolarshice an kamashine bayan da asirinshi ya tonu kuma yarinyar ta bayyana cewa ya mata fyaden kusan fiye da sau 3 kenan kuma idan ta kiya yakan daketa hakanan ma mahaifiyarta kan daketa idan taki amincemai.

Yarinyar ta kara da cewa yana mata fyadenne dan wai gabanta ya bude saboda suna son ta fara yin fim din batsa sannan kuma zasu turata kasar Italiya dan karuwanci.

Labarin da wani me rajin kare hakkin bil'adama, Harrison Gwamnishu ya bayar ta shafinshi na Facebook ya kara da cewa tuni har shiri yayi nisa wajan tafiya da yarinyar birnin Legas dan ta fara fim din Batsa inda kuma daga nan za'a aikata kasar Italiya dan yin aikin karuwanci.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment