Tuesday, 17 September 2019

Dea Gea zai zauna a Man Utd har 2023

Mai tsaron ragar Manchester United David de Gea ya sanya hannu a wani sabon kwantiragi da zai sa ya zauna a kungiyar har zuwa shekarar 2023.
De Gea, mai shekru 28, ya buga wa United wasanni 367 tun da tsohon koci, Sir Alex Ferguson ya kawo shi kungiyar daga Atletico Madrid kan kudi fam miliyan 18 da dubu 900 a shekarar 2011.

Mai tsaron ragar, wadda ya bayyana jin dadin sa ya ce yanzu haka ya kyautata makomarsa kuma burinsa shine ya taimakawa kungiyar ta cimma muradanta.

De Gea, wanda sau 40 ya buga wa kasarsa Spain wasa, ya taimaka wa United ta ci kofin Firimiyar Ingila a kakar wasan 2012/2013, sannan ya ci kofin FA bayan shekaru 3, da kuma kofin League Cup da na gasar zakarun Turai na Europa a kakan wasa ta 2016-17.

Dan kasar Spain din wadda sau da dama an danganta shi da komawa Real Madrid ta Spain yana shekarar karshe ne na kwantaraginsa, wadda da ya ga dama zai tattauna da wasu kungiyoyi kan yiwuwar kula wata yarjejeniya.
RFIhausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment