Friday, 13 September 2019

Don Inganta Tsaro: Za A Dakatar Da Duk Wani Layin Da Ba A Yi Masa Rajista>>Ministan Sadarwan Sheik Pantami

Maigirma Ministan Sadarwa na Nijeriya Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya bayyana cewa akwai layukan kiran waya sama da miliyon tara da dubu dari biyu (9.2 Million) wanda ake amfani dasu ba tare da an musu rijista ba.


Ministan ya yi alwashi cewa za'a dakatar da duk wani layin kiran waya da ba a masa rijista ba, ministan ya umarci hukumar dake lura da harkokin sadarwa wato NCC da ta dauki matakin gaggawa wajen dakatar da duk layukan da ba'a musu rijistan ba

Jama'a irin wadannan layuka da ba'a musu rijista ba sune layukan da 'yan ta'adda musamman masu garkuwa da mutane suke amfani dashe wajen kira don a biya kudin fansa, da irin layukan ne 'yan damfara ke amfani dashi su damfari dunbin al'umma.

Babu shakka wannan mataki da Maigirma Minista ya dauka abune mai kyau da zai inganta tsaron Nigeria, sannan ya taimaka wa jami'an tsaro wajen samun nasara akan masu aikata miyagun laifuka.

Maigirma Minista Allah Ya maka albarka, Ya kara maka taimako da nasara. Amin.

Daga Datti AssalafiyKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment