Sunday, 15 September 2019

Fadakarwa me Muhimmanci: KARUWAR GIDA
Malam Yaseer Gombe Ya Rubuta

Wannan wannan wani babban al'amari ne daya tunkaro gidajen mu wanda ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen tarbiya da addu'a ga 'ya'yansu Allah Ya saita musu su.

Ita wannan karuwar ba'a gidan karuwai take ba, ba kuma zaman kanta take yi ba,  a'a hasalima yawancin su a gaban iyayensu suke, kodai suna Jami'a suna kwana a can ko kuma suna gidan iyayensu.A baya, idan kaji ance wacce karuwa ce, toh zaka same ta a bariki tana sharholiyarta ta kode tana shan taba da wiwi. Amma na yanxu cikin musubin karshen zamani yanmata ne na gida matsakaita wadanda basu wuce shekaru 17-25 suka zama karuwai.

Yarinya ce zaka ganta Kamila da shigan kamala, babu alaman hau ko iskanci tattare da ita, amman ta zubar da kanta ana lalata da ita a lungun unguwarsu, wata a hotel, wata a shago, wata a mota, wata a dakin uwarta, wata a dakin Gayu dake off campus.

Yarinya ce karama yar 14 ko 15 zata sanya uniform na Boko is Islamiyya ammana bazata karasa makaranta ba, sai dai taje ayi zina da ita ta dawo gidansu ta kwana.

Abun haushi abun takaici wallahi da yawan wadannan yara babu alaman yunwa tattare dasu, kudin da ake basu da yawansu idan kaga suturar dake jikinsu kai kasan sunfi karfin wannan kudin.

Kawalai ne maza suke jefa qannenmu mata a irin wannan harkan. Da zarar sunga yarinya ta taso, zaka ji suna ce mata yar shila kamar wata tsuntsuwa, suna zuga ta akan tana da kyau.

Daga nan su qulla alaqa dasu ta hanyar tusa musu qawaye karuwan gidan. Ita wannan yarinyar karuwan gidan, a zahiri kamilica domin ko yan unguwa da yawa basu san tana Iskanci ba saboda yanayin shigarta na kamala.

Wallahi munin karuwar gida yafi na karuwa kilaki mai zaman kanta. Domin da dama sukan je gidan miji da yayan wassu, saboda sukan yi ciki a layi ba tare da iyayensu sun sani ba.

Da yawansu koda sunyi aure matuqar sun saba jin mazaje da yawa na shigarsu basu iya jure zama da miji daya.

Mafita anan:

√ Idan kanada 'ya, Qanwa ko dai wata mace da kakeda iko a Kanta, ka tabbatar kana lura da mu'amalarta, suturar datake sanyawa shin kai ka saya mata? Wayar datake riqewa shin kai ka saya? Perfumes dinta, mayinta duk shin kai ka saya?
Rashin kulawa da wassu buqatun wadannan yara da iyaye keyi musamman kudin kashewa da subs na waya ko ita wayar kanta yakan jefasu wannan harkan.

√ Dole iyaye su dage da nemawa yayansu shiriyar Allah domin Shike shiryar da wanda Yaso

√ Dole ne iyayen dasuka saki layin iyaye da kakanni wajen tarbiyan yaya su koma hakan. Domin zaiyi wuya a baya kasamu yarinya ba'a san ina take zuwa ba kuma dayawa suke alaqa kuma waye mai zuwa wajenta. Ammana yanxu mun waye zakaga yarinya har gidansu tazo da Gaye wai mom ga friend dina na school.

√ Dole iyaye su rage tsangwama da kuma sanyawa yayansu wadatar zuciya da nuna musu Allah Ke komai su kuma riqe mutuncin su

√ Ayi qoqari wajen nunawa yara dogoro da kai ta hanyar koya musu sana'o'in hannu.

Ubangiji muke roqo Ya karemu daga sharrin zamani, Ya kare mana yan'uwanmu Mata daga jin hudubar Shaidan duniya da lahira.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment