Monday, 23 September 2019

Fuskar mata mai shekaru dubu 7,500 a duniya

Masanar kimiyya da fasaha sun sake sarrafa fuskar wata mata da ƙoƙon kanta mai shekaru 7, 500 da aka gano kusa da Gilbraltar wacce ake zaton ‘yar yankin Anatoliar kasar Turkiyya ce.


Rihoto ya nuna cewa an gano ƙoƙon kan ne mai suna ‘Calpeia’ an gano shi ne a cikin wani kogo a shekarar 1996.

Shugaban gidan ajiye tarihi na Gibraltar watau  Manuel Jaen ne ya jagoranci gano lamarin da ya dauki watanni shidda ana aiki ba dare ba rana.

Dangane da kokon kan da aka gano, manasan kimiyya da fasaha sun yi amfani da DNA na Calpeia inda suka yi hasashen yadda fuskar matan zata kasance idan tana raye.

Ferfesa Clive Finlayson, wanda ke aiki a gidan aje kayan tarihin na Gibraltar ya shaidawa kafar yada labaran Gibraltar Chronicle da cewa matar ta yi rayuwa ne a shekarar 5,400 kafin biladiya kuma tana da bakar launi.

Ferfesa Clive Finlayson ya tabbatar da cewa kashi 90 cikin darin kwayoyin halittanta na nuna cewa ‘yar ainihin kasar Turkiyya ce, inda sauran sauran kaso 10 ke nuna cewa  ‘yar mafarautan kauyen Mesolithic ce.
TRThausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment