Sunday, 8 September 2019

Griezmann ya dorawa matarshi laifin barar da bugun daga kai sai gola


Tauraron dan kwallon kasar Faransa, Antoine Griezmann ya barar wa kasar tashi bugun daga kai sai me tsaron gida a wasan da suka buga da kasar Albania na neman kaiwa ga wasan Euro na 2020.A minti 36 da wasa aka samu bugun daga kai sai gola ala kuma baiwa Griezmann wandagwanine wajan buga irin wannan kwallon a kasa da kuma kungiya amma sai bai ci ta ba.

An dai tashi wasan 4-1.

Kuma wannan shine karin farko da Griezmann din ya barar wada kasarshi da bugun daga kai sai Gola.

Bayan an tashi wasan an tambayeshi ko me zaice akan barar da buhun daga kaisai golan da yayi?

Sai ya kada baki yace sun dai yi Nasara amma shima be san dalilin da yasa ya barar da bugun ba amma watakila dan matarshi bata zo kallon wasan bane.

Ya sha alwashin gyarawa anan gaba
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment