Saturday, 7 September 2019

Gwamna Masari Ya Yi Alkawarin Sakin Duk Wani Dan Bindiga Dake Hannun Hukumomi Tsaro

SULHU DA 'YAN BINDIGA

A kokarin sa na karshe hare-haren Yan Bindiga a jihar Katsina ta hanyar yin sulhu, Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya tabbatar wa yan bindiga, cewa zaa sako masu Yan bindiga dake hannu Hukumomi yan Sanda da sojoji da Kuma wadanda ke gidajen kurkuku daban-daban a cikin jihar Katsina, da suke zaman jiran Sharia a kotuna muddin ba a yanke masu hukunci ba.


Gwamna Masari ya bayyana haka ne, a lokacin da yake cigaba da shiga dajin inda barayin suke da sansani a garin Runka, da ke iyaka da dajin Rugu a Karamar Hukumar Safana.

Masari ya kara da cewa haka kuma yan bindiga, dole ku sako duk wani Wanda kuka sace, koina yake ku tabbatar mana da sako mana shi, ba tare da bata lokaci ba. Saboda wannan sulhun duk wanda bai rungume shi ba, ya zama shaidan, to gwamnati za ta yake shi yadda ya kamata. Gwamnati a shirye take ta biya maku dukkanin bukatun ku, wanda ba zai gagare gwamnati ba.

Shima da yake maida jawabi, daya daga cikin shugabannin yan bindiga, Alhaji Abdulaziz Magware ya bayyana cewa wannan sace sacen mutane da kashe-kashen akwai hannun Jami'an tsaro, masarauta Gargajiya da Kuma wasu daga cikin jami'an Gwamnatin shi. Don haka ya kamata Gwamna ya kara Sanya ido sosai akwai bara-,gurbi a cikin su.

Abdulaziz ya yi kira ga Gwamnan jihar Katsina, Masari da ya gina masu Makarantu da  za su Sanya yaransu, ruwan sha da kuma kayan more rayuwa. Kuma sun yi alkawarin yin sulhu na Amana, muddin aka cika mana wadannan Alkawurran da Gwamna ya dauka.

Da yake jawabi a madadin Jami'an tsaro da ke aiki a jihar Katsina, Kwamishinan Yansanda na jihar Katsina, CP Sanusi Buba ya ce muna goyan bayan wannan sasasanci da sulhu da Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, Kuma za mu bada duk guddummuwar da ta dace don ganin an samu nasara.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment