Friday, 13 September 2019

Gwamnan Bauchi Ya Jajanta Kan Kisan 'Yan Shi'a Da Aka Yi A Bauchi

Gwamna Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi, ya jajanta kan kisan 'yan Shi'a a Bauchi tare da nuna alhini kan al'amarin. Lamarin daya auku ranar Talata lokacin da 'yan Shi'an suka fito Muzaharar Ashura na juyayin kisan Jikan Annabi (SAW) wato Sayyidina Hussaini.


Al'amarin ya yi sanadiyar rasa rayukan 'yan shi'a maza tare da jikkita wasu da kama wasu.

Da yake jawabi lokacin taron jana'izar su Shugaban 'yan shi'an na Bauchi, ya bayyana cewa "Gwamna ya tura da sakon ta'aziyya gare mu tare da nuna alhini kan al'amarin kuma ya bayyana suna cigaba da daukan matakin hakan be sake faruwa ba", inji shi.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment