Tuesday, 10 September 2019

Gwamnan jihar Rivers ya taka 'yancin dan Adam>>Bala Lau

RUSA MASALLACI

Shugaban Kungiyar IZALA Ash-Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya bayyana rushe masallaci da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yayi a matsayin take ' yancin musulmai da neman tayar da fitina a cikin al'umma.


Sheikh Bala Lau ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi lambar yabo daga tawagar ' yan jaridar 'The Reporters' a ofishin kungiyar Izala dake birnin tarayya, Abuja.

Sheikh Bala Lau yace jihar Ribas jiha ce da take dauke da Al'umman musulmai, kuma tsarin mulkin Nijeriya ya baiwa kowa daman yayi addinin sa. Yace babu dalilin da zai sa gwamna ya rushe masallaci.

A saboda haka ne Shehin malamin yayi kira ga gwamnan da ya kiyayi tozarta musulmai ta hanyan rushe wurin ibadar su, saboda hakan ba komai zai kawo ba illa fitina a kasa.

Jaridar 'The Reporters' ta karrama Sheikh Bala Lau ne a matsayin malami mafi bada gudunmawa ga zaman lafiyar kasa da kuma cigaban ta.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment