Tuesday, 10 September 2019

Gwamnan Katsina ya saka hukuncin kisa kan duk wanda ya kaiwa Fulani hari a jihar

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce daga yanzu duk mai aikin sa-kai din da aka kama ya kai wa Fulani hari a Katsina "hukuncin kisa" za a yanke masa.


Masari yana ya yi wannan kalaman ne game da koke-koken da Fulanin suka gabatar wa gwamnatinsa a wata hira ta musamman da BBC.

Daga cikin korafin da suka yi, in ji Masari, shi ne cewa "jami'an tsaro na wulakanta su a cikin daji da kuma amshe masu dukiya".

"Sai kuma 'yan sa-kai da suke hana su shiga kasuwanni, matansu kuma a hana su tallan nono," Masari ya shaida wa BBC.

Bisa wannan dalili ne gwamnan ya ce a yanzu sun dauki matakin hana kai wa Fulanin irin wadannan hare-hare.

"'Yan sa-kai dai mun dakatar da su kuma duk wanda ya taba wani Bafulatani har ya yi sanadiyyar rasa ransa to hukuncin kisa za a yanke masa."

A watan Agusta ne gwamnatin Katsina ta bayar da sanarwar cewa za ta yi sulhu da Fulani masu garkuwa da mutane.

Mai magana da yawun Gwamna Masari Audu Labaran ya ce gwamnan ne zai shiga daji da kansa domin yin sulhun.

"Mun umarci shugabannin kananan hukumomi cewa duk Bafulatanin da zai fita da shanu su ba su takarda a rubuce, kuma shugaban karamar hukuma ne kadai zai saka hannu, in ya so ma ga jami'in tsaron da zai tare su ya karbi wani abu a hannunsu.

"Su kuma (Fulani) kar mu kara ganinsu da bindiga zuwa wani gari kafin mu fara kashi na biyu na karbe bindigogin da ke hannunsu," in ji gwamnan .Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment