Friday, 13 September 2019

Gwamnati zata fitar da 'yan Najeriya Miliyan 100 daga talauci cikin shekaru 10>>Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fadi cewa gwamnatinsu ta saka manufar fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga talauci nan da shekaru goma masu zuwa.
Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakane a yayin da ya kaiwa me martaba sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar ziyara a faradarshi a ziyarar dabya kai jihar Kebbi.Ya bayyana cewa abinda ya kaishi jihar shine taimakawa masu kananan sana'o'i da kuma duba gyaran kasuwar da aka ti data kone, sa kuma kaddamar da tallafin kananan 'yan kasuwa na Tradermoni wanda ake lamuncewa karamin dan kasuwa har zuwa Naira dubu 100.

Osinbajo yace a ziyarar da ya kai kasuwa ya hadu da wata mata me sayar da kayan miya inda ta gayamai cewa, jarinta Naira 500 ne kawai, yace to irin wannan matarce suke maganar tallafawa da dubi 10.

Yace suna da tsarin fitar da 'yan najeriya Miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekaru 10 masu zuwa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment