Sunday, 8 September 2019

Gwamnatin jihar Rivers ta dakatar da aikin hukumar jin dadin Alhazan jihar

Gwamnatin jihar Rivers ta dakatar da hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar saboda yanda ake gudanar da ayyukan hukumar akwai kumbiya-kumbiya a ciki.
Mataimakin shugaban kungiyar Jama'au Nasril Islam, Alhaji Abubakar Orlu ne ya bayyana haka jiya a jihar Rivers a ganawar da yayi da Manema labarai inda yace kuma gwamnatin jihar bata ruguza masallaci ba.

Yace a baya wasu miyagun ma'aikata sun rika kai kujerun hajjin jihar zuwa wata jiha dan hakane gwamnatin jihar ta dakatar da aikin hukumar.

Game da Rusa masallaci kuwa,Orlu yace wasu mutanene kawai suka so hada musulmai da kiristoci fada da kuma bata sunan gwamnan jihar, Nyesom Wike,kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment