Tuesday, 17 September 2019

Hankalin mazauna Abuja ya tashi game da satar mutane

A Najeriya, hankalin wasu mazauna Abuja, babban birnin kasar ya fara tashi sakamakon matsalar satar mutane da ta fara yawaita a birnin.


Rahotanni dai na nuna cewa akalla mutum biyar ne aka sace a cikin mako guda a birnin, ciki har da 'yar wani babban dan siyasa.

Sai dai mahukunta na tababa a kan alkaluman, suna zargin kambama matsalar ake yi.Matsalar satar mutane dai ba wani sabon al'amari ba ne a wasu sassan Najeriya da dama, da kuma baki dayan jihohin da suka yi wa Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya kawanya.


Wannan matsalar ce ma ta sa mutane da dama, musamman masu sukuni ke kaurace wa hanyar motar Abuja zuwa Kaduna, ciki har da manyan jami'an tsaro da manyan ma'aikatan gwamnati.

A yanzu al'umma sun fi aminta da bin jirgin kasa domin sufuri tsakanin manyan biranen biyu masu makwaftaka da juna.

Sai dai a dan tsakanin nan matsalar satar mutanen ta kunno-kai cikin babban birnin tarayyar, har ta kai ga wasu unguwanni na masu hali.


Wani dan siyasar ya wallafa maganar satar diyarsa a shafinsa na sadarwa na intanet, inda ya nemi a taya shi da addu'a.

Kodayake daga baya ya sake wallafa labarin sakin 'yar tasa, amma bai ce komai a kan yadda aka yi aka ceto ta ba, duk kuwa da cewa wasu rahotanni na cewa sai da aka biya makudan kudade.

Faruwar wannan al'amari ya yi sanadin yaduwar wasu bayanai ta kafafen sada zumunta na intanet, inda wasu ke cewa matsalar satar mutanen karuwa take yi a Abuja.

Lamarin da ya fara tayar da hankalin jama'a.

A wasu wuraren an rinka tashi a masallatai da wuraren ibada ana jan hankalin mutane da su rinka lura sosai domin gudun abin da ka iya faruwa na satar yara har ma da manyan.

Kafafen yada labaru ma a cikin 'yan kwanakin nan sun rinka tattaunawa kan wannan matsala.

A birnin na Abuja, akwai lokacin da aka girke kemarorin tsaro a bangarori daban-daban na birnin.

An yi hakan ne da nufin inganta tsaro, amma bincike ya nuna cewa haka mafi yawa suka yi batan-dabo.


Sai dai rundunar 'yan sandan Najeriya, a wata sanarwar da ta aika wa BBC da wasu kafafen sadarwa, ta bayyana cewa ana kambama tabarbarewar tsaron da ake fuskanta a Abuja da yawaitar satar mutanen da ake magana, "alhali birnin tarayyar na daga cikin biranen duniya da za a iya cewa miyagun laifukan da ake aikatawa a cikin su da sauki."

Amma rundunar ba ta fito ta musanta sace diyar dan siyasar da aka yi ba.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment