Monday, 9 September 2019

Harin Kyamar Baki: An kashe mutane 2 a sabon rikici a kasar Afrika ta Kudu

A wani sabon rikici daya aka yi a kasar Afrika dake da alaka dana kyamar Baki an samu rahoton kisan mutane 2.

Rikicin dai ya farane a birnin Johannesburg inda wani dan siyasa yayi taro da matasa yake kuma bayyana musu rashin jindadinshi kan hare-haren kyamar bakin da ake kaiwa saboda suna bata sunan kasar ta Afrika ta kudu a idon Nahiyar Afrika.

Saidai a lokacin da dan siyasar ke bayani mutane sun fara ficewa daga gurij taron inda wasu suka rika mai ihun bamaso.

Daga nanne sai matasan suka bazama cikin gari aka kona wasu shaguna ciki hadda na 'yan kasar ta Afrika ta kudu, kamar yanda BBC ta ruwaito.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment