Sunday, 15 September 2019

Harin 'yan Houthi ya rage man Saudiyya da ganga miliyan 5

Sadiyya ta rage yawan man da take fitarwa kasuwannin duniya sakamakon hare-haren da 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka kai wa matatun mai biyu mallakin gwamnatin kasar, wato Aramco.


Hare-haren jirage marasa matuka guda biyu na 'yan tawayen sun tilasata wa Saudiyya rage yawan man da take fitarwa da ganga kusan miliyan shida.

Yanzu Saudiyya ta koma fitar da kimanin rabin adadin man da ta saba fitarwa kasuwannin duniya, a cewar kamfanin dillanci labaru na Reuters da WSJ.

Jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, ya bayyana matukar damuwa gme da harin inda ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke yakar juna a kasar Yemen su bi a hanakali.

Hoton da wani gidan talabijin ya yada, ya nuna gobara na ci a matatar mai mafi girma mallakin kamfanin Aramco wato Abqaiq.Daya gobarar kuma ta tashi ne a filin hakar mai na Khurais, sakamakon hare-haren da jirgare marasa matuka suka kai a wajen.

Gwamnatin Saudiyya na jagorantar rundunar hadin gwiwa da ke goyon bayan gwamnatin Yemen, yayin 'yan tawayen Houthi ke samun goyon baya daga kasar Iran.


Wani kakakin 'yan tawayen Houthi, Yahya Sarea, ya ce sun yi amfani da jirage marasa matuka 10 a harin.

Sarea, wanda ke zaune a birnin Beirut na kasar Labanan ya yi barazanar za su kara kai wa Saudiyya wasu hare-haren.

Ba a samu cikakken bayani a kan yawan barnar da wutar ta yi ba, kuma hukumomin Saudiyya ba su ce komai game da abin da suke ganin ya haifar da kai harin ba.

Amma kamfanin yada labarai na kasar ya ce jami'an kwana-kwana sun yi nasarar shawo kan wutar da ta tashi sakamakon harin da aka kai a Abqaiq da Khurais.

Amma mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ta Saudiyya, Mansour al-Turki, ya ce ba a rasa rai a gobarar ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na AFP ya ruwaito.

Dakarun Saudiyya sun dakile harin kunar bakin wake da kungiyar Alqeada ta nemi kai wa Abqaiq a 2006.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment