Wednesday, 11 September 2019

Hukumar Tace Finafinai Ta Jihar Kano Ta Kama Mawaki Nazir M. Ahmad

DA DUMIDUMINSA

Rahotanni daga jihar Kano sun tabbatar da cewa hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta kama mawaki Nazir M. Ahamd bisa zargin sa da sakin wata wakar da hukumar ba ta tantance ba.


Majiyar ta bayyana cewa wakar da aka kama mawaki Naziru saboda ita, ta kai kimanin shekara uku zuwa hudu da sakinta.

Saidai wasu na ganin kamun da aka yi wa Sarkin mawakan na Sarkin Kano, ba ya rasa nasaba da wata talla da ya yi wa dan takarar gwamnan Kano karkashin PDP, Abba Kabir Yusuf.
Rariya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment