Wednesday, 18 September 2019

Ina son in ci karin Ballon d'Or dan in fi Messi in zama na Daya a Duniya>>Ronaldo

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa yasan bajintar da yayi a Kwallo tasa ya shiga tarihin ta da baza'a manta dashi ba.Saidai Ronaldo yace ya kamata yaci karin kyautar gwarzon dan kwallo ta Duniya, Ballon d'Or dan kuwa ya cancanci hakan, yace Messi gwanin dan kwallone babu ja akan wannan duk da dai su ba abokai bane amma suna da kyakkyawar fahimta kuma wasu zasu ce Ronaldonne na daya a harkar kwallo amma wasu zasuce wani ne shine na biyu wannan duk be dameshiba.

Yace burinshi shine ya ci karin Kyautar Ballon d'Or ta shida ta bakwai ko ta takwas ta yanda zai shiga gaban Messi a matsayin dan kwallon da babu kamarshi.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment