Wednesday, 11 September 2019

Jami'an kasar Afrika ta kudu sun kafa shingen hana Dawo da 'Yan Najeriya gida

A yayin da ake jiran 'yan Najeriya da aka tura jirgi ya daukosu daga kasar Afrika ta kudu, an fara samun damuwa bayan da aka ji shiru babu duriyarsu a yayin da ya kamata ace sun sauka a Najeriya.Wannan yasa jaridar The Nation ta tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake kasar ta Afrika ta kudu dan jin me ya kawo tsaikon dawo da 'yan Najeriyar gida?

Wani jami'in ma'aikatar da be bayyana sunanshi ba yace jami'an shige da fici na kasar ta Afrika ta kudune ke basu matsala, basa so a kwaso 'yan Najeriyar zuwa gida, da suka ga an kwaso 'yan Najeriyar za'a tafi dasu sai suka kafa shingen bincike.

Sun fara binciken takardun tafiya, suka ga kowa yana dashi, ofishin jakadancin Najeriyar ya samarwa duk wani dan Najeriya da za'a dawo dashi cikakkun takardun tafiya, sai kuma jami'an na kasar Afrika ta kudu suka koma binciken ta yanda aka yi 'yan Najeriyar suka shiga kasar ta Afrika ta kudu.

Majiyar ta ci gaba da cewa mutane 182 ne kawai cikin 320 jami'an kasar ta Afrika ta kudu suka ba bari suka shiga jirgin amma suna ta kama 'yan Najeriyar inda suke zarginsu da shiga kasar ba tare da izini ba. Ya kara da cewa jirgin na kunne yana ta kona mai, kasar Afrika ta kudu bata so ace 'yan Najeriya na kwashe mutanensu daga kasar.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment