Tuesday, 10 September 2019

Jami'an tsaro sun budewa 'Yan Shi'a wuta a Kaduna, Sokoto, Bauchi da Katsina, Mutum 3 sun mutu

Rahotanni daga jihohin Katsina da Kaduna, Bauchi da Sokoto sun bayyana yadda jami'an tsaron Nijeriya suka bude wuta kan 'yan Shi'a Almajiran Sheikh Zakzaky a yayin gudanar da Muzaharar Ashura ta duniya a yau Talata.


A Kaduna wakilin mu ya tabbatar mana da cewa an kashe akalla mutane uku, yayin da aka harbi gommai, kafin watsewar taron.

A Katsina ma wani abu mai kama da hakan ya faru inda jami'an tsaro suka kame wasu tare da tarwatsa taron. Ga wasu daga hotunan.
Rariya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment