Tuesday, 24 September 2019

Ji Abinda Ronaldo yace bayan da Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon FIFA 2019

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo be halarci wajan bayar da kyautar FIFA da aka yi jiya ba wadda Messi ya dokeshi ya lashe kyautar ta tauraron dan kwallon FIFA ta 2019, wasu na ganin watakila Ronaldon ya samu labarin cewa ba shi za'a baiwa kyautar ba shiyasa.
Wannanne karo na 2 a jere da Ronaldon ya ki halartar bayar da kyautar ta FIFA.

Saidai Ronaldon ba zai buga wasan da Juventus zata buga ba na yau da kungiyar Brescia saboda ciwon da yake dashi, wasu na tunanin watakila abinda ya hanashi zuwa bayar da kyautar ta jiya kenan.

Bayan baiwa Messi kyautar ta tauraron FIFA, Ronaldo ya saka hoton sama inda yake danna Ipad dinshi ya kuma rubuta sako me cewa:

Hakuri da juriya ne abubuwan da suka banbanta gwanaye da masu koyo, duk wani babban abu da kadan-kadan ya fara. Baka iya yin komai, amma ka yi dukkan me yiyuwa dan ganin ka cimma burinka. Kuma ka sa a ranka cewa komin duhun dare gari zai waye.

Wasu dai sun yabawa Ronaldo yayin da wasu suka caccakeshi kan cewa maimakon wannan surutu da yayi kamata yayi ace ya taya Messi murna.

A damar da aka baiwa kowane dan wasa ya zabi gwaninshi dan tantance wanda za'a baiwa kyautar ta gwarzon dan kwallon FIFA, dama kowane dan wasa ana bashi damar zabar 'yan wasa 3 ne, Messi ya zabi Ronaldo amma Ronaldo be zabi Messi ba.

Messi ya zabi Sadio Mane da Ronaldo da Frankie De Jong. Shi kuwa Ronaldo Matthijs De Ligt da Frankie De jong da Mbappe ya zaba. Shi kuwa Van Dijk da yazo na biyu a FIFA ya zabi Messi ne a matsayin na farko sai Mohamed Salah sai Sadio Mane.

Hazard kuwa ya Zabi, Sadio Mane, Van Dijk da Messi, shi kuwa Luka Modric ya zabi Tonaldo a matsayin na farko sai Aubameyang a matsayin na biyu sannan Xhaka a matsayin na ukunshi.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment