Sunday, 8 September 2019

Ji abinda wakilin da shugaba Buhari ya aika kasar Afrika ta kudu ya gayawa shugaban kasar

Me magana da yawun shugaban kasar Afrika ta kudu, Khusela Diko ya bayyanawa kamfanin dillancin Najeriya, NAN tattaunawar da wakilin da shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya tura kasar kan harin kyamar baki da ake kaiwa kan 'yan Najeriya.Diko ya bayyanawa NAN cewa wakilin na Najeriya ya tabbatarwa da kasar Afrika ta kudu cewa Najeriya na nan kan tsarin ganin an ciyar da nahiyar Afrika gaba wanda itama kasar Afrika ta kudun ta mince dashi.

Ya kara da cewa ya kuma tabbatarwa da kasar Afrika ta kudun cewa Najeriya zata yi kokarin ganin baiwa kasuwancin kasar Afrika ta Kudu dake Najeriya kariya dan ganin ba a kai musu hari ba.

Shima shugaban kasar Afrika ta kudun, Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa zai baiwa 'yan  Najeriya da kuma kasuwancin su dake zaune a kasar ta Afrika ta kudun kariya.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment