Wednesday, 11 September 2019

Ji martanin gwamnan Kaduna yayin da wani ya ce mai Makaryaci

A jiyane rahotanni suka watsu cewa gwamnan jihar Kaduna,Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi gargadin cewa duk wanda zai yi wani rubutu a dandalin Twitter a akan jihar Kaduna to ya kula dan kada ya watsa labaran karya da zasu kawo tashin hankali a jihar, Gwamnan ya kara da cewa duk wanda yayi haka to suna da dokar da zata kamoshi.Bayan wannan sanarwa ne sai wani me suna chuks Akunna ya kalubalanci gwamnan inda yace, Gwamna El-Rufai yayi gargadin cewa zai yi maganin wanda basa kiyayewa idan zasu yi magana akan gwamnatinshi. To Gani. Ta yaya gwamnan zai yi alkawarin samar da ayyuka dubu 50 a yayinda kamfanin da yayi hadin gwiwa da shi, Arla Foods gaba dayan ma'aikatanshi basu kai mutum dubu 20 ba? Ya karkare da kiran gwamnan da Makaryaci.

A martaninshi ga wannan mutum, gwamna El-Rufai ya bayyana cewa, Cewa mutum makaryaci hadda ni, El-Rufai ba laifi bane a jihar Kaduna. Abinda zaka yi ka jawo hankalinmu kanka shine saka hotuna, ko bidiyo ko wasu kalamai na karya da zasu kawo matsalar zaman lafiya a Kaduna. Ka gwada ka gani.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment