Sunday, 15 September 2019

Ji yanda Hira ta kaya tsakanin wasu iyaye da 'ya'yansu


Yara manyan gobe, me baiwa gwamnan Kano shawara akan sadarwa, Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu a shafin Twitter ya bayar da labarin yanda wataran yana Saudiyya ya kira gida.Yace sai ya bukaci a bashi karamin danshi su gaisa sai, da yaron ya amsa sai ya tambayeshi, baba Kana ina? Sai yace mai Ina dakin Allah. Sai yaron yace, Ka bani shi mu gaisa.

Bayar da wannan labarin ke da wuya sai wani shima ya bayar da labarin nashi dan inda yace shima wataran suna tafiya zuwa Masallaci da dan nashi sai suke maganar inda Allah yake, sai yace mai Allah yana sama, sai dan nashi daga kai yace mai daidai ina?

Hakanan shima wani ya bayar da labarin cewa 'yar uwarshi ta kammala Alwala sai tace bari ta je ta gaishe da Allah, karamar kanwarta dake kusa sai tace mata jirani muje ina so in ganshi.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment