Saturday, 7 September 2019

Jirgi dauke da mahajjata 600 yayi hatsarin, ya Sauka a Naija

Wani jirgin sama da ya taso daga kasar Saudiyya dauke da mahajjata zuwa Najeriya yayi hatsari inda yayi saukar gaggawa a filin tashi da saukar jirage na jihar Naija.Rahoton The Nation yace wani ma'aikacin filin jirgin ya bayyana cewa matsalace aka samu a injin jirgin daya tilasta saukar gaggawa kuma jirgin ya lalace.

Mahajjata 600 ne ke cikin jirgin kuma cikin ikon Allah babu ko daya daya rasu ko kuma ya ji rauni.

Wani ma'aikacin filin jirgin na Naija ya bayyanawa jaridar cewa banda Allah ya tsare da ace jirgin ya kama da wuta da duk sai filin jirgin ya kone dan basu da kayan kashe gobara.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment