Wednesday, 18 September 2019

Jirgi na 2 da zai kwaso 'yan Najeriya ya sauka a Afrika ta kudu


Shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, Abike Dabiri Erewa ta bayyana cewa jirgin Air Peace a karo na biyu ya sauka a kasar Afrika ta kudu dan dawo da 'yan Najeriya kaso na biyu dake son dawowa daga kasar.Akwai 'ya  Najeriya a kasar ta Afrika ta kudu da hare-haren kyamar baki ya ritsa dasu wanda kuma auke aon dawowa gida Najeriya.

A sanarwar data fitar ta shafinta na Twitter, Dabiri Erewa ta bayyana cewa, jirgin ya sauka a kasar Afrika ta kudu kuma bayan tabbatar da takardun tafiya da binciken jami'an shige da fici na kasar ta Afrika ta kudu zai kwaso 'yan Najeriya zuwa gida.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment