Saturday, 14 September 2019

Kalli bidiyon da Mo Salah ya saka na abin dariya tsakninshi da Mane

A yayin da Liverpool ke shirin haduwa da kungiyar Newcastle United a yau, Asabar bayan dawowa daga hutun gasar Premier League, Magoya bayan kungiyar sun zuba ido suga yanda zata kaya tsakanin Mo Salah da Sadio Mane bayan da Mane ya nuna fushinshi karara kan rashin bashi kwallo da Salah yayi a wasansu da Burnley da suka tashi 3-0.


Saidai dan ya nuna cwa babu wata matsala tsakainshi da abokin wasanshi, awanni kamin fara wasan, Mohamed Salah ya saka wani bidiyon yara da ya watsu sosai inda suka hadu suka rungume juna, saidai a bidiyon da Salah din ya saka an canja kawunan yaran dana Salah da Mane sai kuma wani babban mutum dake kusa dasu aka saka kan Kocin Liverpool, Jurgen Klopp.

Abin ya dauki hankula sosai:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment