Wednesday, 18 September 2019

Kalli bidiyon kwallon da Barkley ya bararwa da Chelsea, Saidai Lampard ya goyi bayanshi

 Bayan zubar da kwallon da yayi, Ross Barkley ya samu kariya daga me horas da 'yan Wasan Chelsea, Frank Lampard inda ya bayyana cewa dama can idan yana cikin fili shine ke buga bugun daga kai sai gola.
Bayan wasan na jiya da Chelsea ta sha ci daya me ban haushi daga Valencia kuma ta samu damar rama cin amma Barkley ya barar da damar an tambayi Lampard shin ba Jorginho ko Willian ya kamata ace daya daga cikinsu ya buga bugun daga kai sai golan da aka samu ba?

Ya kada baki yace, dama can idan dai Barkley na cikin fili to shine ke yin bugun daga kai sai gola. Ya kara da cewa amma ya buga bai ci ba dan haka rashin sa'ane, Lampard yace sun yi kokari saidai kawai basu da sa'a ne.

Anga dai Willian da Jorginho suna magana da Barkley kamin ya buga kwallon inda da yawa suka fassara cewa sun ce ya barsu su bugane amma yace su bar mai zai buga.

An tambayi Lampard ko me Willian da Jorginho ke gayawa Barkley? Amma ya bayar da amsar cewa be sani ba.

Kalli bidiyon kwallon da Barkley ya barar:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment